ABNA24 : A jiyan ne aka iso da gawar mirigayin daga Amurka.
An yi masa jana’iza ne a babban Masallacin Kuwait, inda danginsa da manyan jami'an gwamnati suka yi masa sallar.
Sheikh Sabah ya rasu ne a ranar Talata a Amurka, bayan fama da doguwar jinya, bayan kwantar da shi a cikin watan Yuli.
Kasashen duniya da dama dai sun aike wa kasar ta Kuweit da sakon ta’aziyyar rasuwar sarkin.
Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta aike wa Kuwait da sakon ta’aziyya kan rasuwar sarkin kasar Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah.
Iran Ta Mika Sakon Ta'aziyya Ga Kuwait Game Da Rasuwar Sarki Al-Sabah
A wani sako da ya aike wa kasar, ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya ce, ya kadu da jin labarin rasuwar sarkin na Koweit, tare da yi masa fatan Allah ya jikansa.
Mista Zarif, ya danganta mirigayin da mutum na gari mai son ci gaba kasarsa dama yankin baki daya.
Haka kuma Iran, ta yi wa Kuwait da al’ummarta fatan alhairi, da samun ci gaba da kwanciyar hankali karkashin sabuwar sarautar.
342/